Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Bola Ahmad Tinubu da mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III da ragowar wasu manya ‘yan Nijeriya a kasar Saudiyya a lokacin wani taron shan ruwa.
Ganawar dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ya rage kwanaki kadan a rantsar da Buhari a matsayin zababben shugaban Nijeriya a karo na biyu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa malam Garba Shehu ya fitar, ya ce Tinubu ya yi amfani da damar shan ruwan ne domin yin kira ga shugabannin Nijeriya su guji furta kalaman da za su iya haddasa fitina a kasa.
Daga cikin wadanda suka halarci taron shan ruwan sun hada da sarkin Kazaure Najib Hussaini Adamu da ragowar wasu hadiman shugaba Buhari da wakilan gwamnati da ke cikin tawagar shugaban kasa.

You must log in to post a comment.