Home Labaru Samar Da Tsaro: Kwamishinan ‘Yan Sandan Bauchi Ya Ziyarci Helkwatar NUJ Da...

Samar Da Tsaro: Kwamishinan ‘Yan Sandan Bauchi Ya Ziyarci Helkwatar NUJ Da Ke Bauchi

258
0

Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Bauchi da Rundunar ‘yan sandan jihar sun yi wata ganawa domin shawo kan kalubalen rashin tsaro da ake fuskanta a jihar baki daya.

Ganawar dai, na zuwa ne bayan wata ziyarar neman goyon baya da sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Habu Sani Ahmadu ya kai sakatariyar ta kungiyar ‘yan jaridu ta NUJ da ke jihar bauchi.

Shugaban kungiyar ‘yan jaridun Kwamared Ibrahim Malam Goje da ya ke jawabi a lokacin ziyarar, ya kasancewar su daya daga cikin masu ruwa da tsaki wajen shawo kan matsalar tsaro za su bada ta su gudummawa wajen ginin an kai ga samun nasarar a jihar da ma kasa baki daya.

A nashi bangaran Habu Sani ya shaidawa ‘yan jaridun cewa, rundunar ‘yan sandan jihar zata tabbatar ta yi aiki da manema labarai domin samar da kyakyawar alaka tsakanin ‘yan sanda da’yan jarida da sauran al’ummar gari domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al’ummar jihar.

A karshe Habu Sani ya bukaci ‘yan jaridu su yi amfani da kwarewa rsu wajen taimaka wa jami’an tsaro domin kawo karshen ta’addanci tare da fatan manema labarai za su bashi cikakken hadin kai da kuma goyon baya.