Home Labaru Ta’addanci: An Yi Ba-Ta-Kashi Tsakanin ‘Yansanda Da ‘Yan Bindiga A Kaduna

Ta’addanci: An Yi Ba-Ta-Kashi Tsakanin ‘Yansanda Da ‘Yan Bindiga A Kaduna

405
0

Rayuwar wani jami’in dansanda ta salwanta, yayin wata musayar wuta da aka kwashi tsawon lokaci ana yi tsakanin wasu gungun ‘yan bindiga da su ka kai hari kamfanin gine gine na Mothercat da ke garin Kaduna.

Lamari dai ya faru ne a unguwar Mando, inda ‘yan bindiga su biyar su ka kaddamar da hari a kamfanin da misalin karfe 5:40 na safiyar Larabar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun yi kokarin kutsawa cikin kamfanin ne da nufin sace wasu turawa da ke aiki a kamfanin domin yin garkuwa da su.

Sai dai ‘yan sandan da ke gadin kamfanin ba su yi kasa a gwiwa ba, inda su ka tarbi ‘yan bindigar aka yi ta musayar wuta, har su ka kashe ‘yan bindiga uku, yayin da biyu su ka tsere sannan dan sanda guda ya rasa ran sa.‘Yan sandan sun ce, sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku, da boma-bomai da tabarau na musamman don rufe idanun wanda su ka kama da kuma motar da su ka kai harin da ita kirar Golf.

Leave a Reply