Home Labaru Kiwon Lafiya Kandako: Jabun Maganin Kwalara Ya Karade Kasuwannin Nijeriya – NAFDAC

Kandako: Jabun Maganin Kwalara Ya Karade Kasuwannin Nijeriya – NAFDAC

400
0
Moji Adeyeye, Shugabar Hukumar
Moji Adeyeye, Shugabar Hukumar, NAFDAC

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magungunan ta kasa NAFDAC, ta yi kira ga mutane da ma’aikatan kiwon lafiya a maida hankali a kuma kula, domin akwai wani maganin Amai da gudawa na jabu da ya karade kasuwannin Nijeriya mai suna ‘Dukoral’

Shugabar hukumar Moji Adeyeye ta yi wannan kira a Abuja, inda ta ce tuni maganin ya bazu a kasuwannin kasar Bangladesh.

Adeyeye, ta ce hukumar NAFDAC ta samui tabbacin haka ne daga Kungiyar kiwon lafiya ta duniya da ke kasar Bangladesh, bayan ta gudanar da bincike a kan ingancin wannan magani.

Ta ce magani ya na dauke ne da rubutun harsunan Turanci da Faransanci, sannan kamfanin sarrafa magunguna na Valneva Canada ne ya sarrafa shi, amma bincike ya tabbatar da cewa kamfanin Valneva Canada ba shi ne ya sarrafa maganin ba.Adeyeye, ta bukaci duk masu shigo da maguguna daga kasashen wajen su rika sa ido matuka, kuma mutane da ma’aikatan kiwon lafiya za su iya tuntubar ofishin hukumar mafi kusa domin sanar da su idan aka yi kicibis da wannan jabun magani

Leave a Reply