Home Labarai Sultan Ya Buƙaci Ƴan Najeriya Su Daina Tsine Wa Shugabanni

Sultan Ya Buƙaci Ƴan Najeriya Su Daina Tsine Wa Shugabanni

33
0
Sa'adu Abubakar Sultan of Sokoto (1)
Sa'adu Abubakar Sultan of Sokoto (1)

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga ƴan Najeriya su riƙa yi wa shugabannin ƙasa addu’a duk yanayin da ake ciki, kuma duk yanayin da ƙasa ke ciki.

Sultan Abubakar na III ya yi wannan kiran ne a Jami’ar Ilorin a ranar Alhamis a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron ƙaddamar da littafin da aka rubuta a kan shugaban hukumar JAMB Farfesa Is’haq Oloyede, wanda ya yi ritaya daga aikin jami’a.

Mai alfarman ya ƙara cewa, a daina tsine wa shugabanni duk yadda abubuwa suka lalace, maimakon haka gara a riƙa yi musu addu’a,  kuma a daina faɗin abubuwa marasa kyau a kan su domin duk lalacewar shugaba bai kamata arika tsine masa ba.

A nasa jawabin, ministan shari’a Lateef Fagbemi (SAN), wanda shi ne shugaban taron, ya yi kira ne ga ƴan Najeriya su riƙa ƙarfafa wa shugabannin su gwiwa.

Leave a Reply