Home Labarai Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Babu Gibin Shugabanci Duk Da Cewa Tinubu...

Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Babu Gibin Shugabanci Duk Da Cewa Tinubu Da Shetima Basa Kasa

34
0
Tinubu Rejoices
Tinubu Rejoices

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce ba za a samu giɓin shugabancin ƙasar ba duk da cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima ba sa ƙasar.


Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara a kan watsa labarai,

Bayo Onanuga ya fitar  inda ya ce bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya tafi Sweden domin ziyarar aiki, alhalin Tinubu bai dawo ƙasar daga hutun mako biyu da ya tafi ba.


Ya ce yakamata a gane cewa shugaban ƙasa da mataimakinsa suna cigaba da gudanar da ayyukansu, ko da ba sa ƙasar.


Shugaba Tinubu ya bar ƙasar nan ne a ranar 3 ga Oktoba, inda ya je hutun mako biyu, amma duk da haka bai daina gudanar da harkokin shugabanci ba, kuma ya kusa dawowa ofis.


Mataimakinsa kuma  ya tafi  kasar Sweden amma sauran ɓangarorin gwamnati kamar shugaban majalisar dattawa da sakataren gwamnati da ma’aikatu da da manyan hafsoshin tsaro kowa na cigaba da aiki yadda ya kamata.


Ya ce ko a zamanin mulkin Muhammadu Buhari an samu haka, inda shugaba da mataimakinsa suka bar ƙasar, “lokacin da Buhari ya je taron MDD 77, shi kuma mataimakinsa ya halarci birne Sarauniyar Ingila Elizabeth II.

Leave a Reply