Home Labaru Sufurin Sama: Hukumar Faan Ta Rufe Filayen Jiragen Jihohin Gombe Da Kebbi...

Sufurin Sama: Hukumar Faan Ta Rufe Filayen Jiragen Jihohin Gombe Da Kebbi Saboda Bashi

439
0

Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya FAAN, ta rufe filayen sauka da tashin jirage na jihohin Gombe da Kebbi saboda bashin da ake bin su da ya haura Naira Miliyan 800.

Rufe filayen sauka da tashin jiragen dai zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayu na shekara ta 2019.

A cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce za ta janye jami’an kiyaye gobara da masu gadi da tsaro a filayen jiragen saman biyu.

Tun cikin makonni biyu da su ka gabata ne, hukumar ta aike da sakon gargadi ga gwamnatocin jihohin biyu amma su ka gaza biyan basusukan da ake bin su.

Bincike ya nuna cewa, hukumar FAAN ta ba gwamnatocin jihohin biyu isasshen lokaci domin su biya basussukan amma su ka ki aikata hakan.

An dai gano cewa, hukumar za ta cigaba da bibiyar sauran filayen sauka da tashin jirage na wasu jihohin da ake bi bashi bayan ta rufe na jihohin Gombe da Kebbi.

Leave a Reply