Hadadaiyar kungiyar Kwadago ta Nijeriya, ta ce ba za ta amince da karin farashin man fetur da harajin kayayakin masarufi ba, yayin da su ke kira ga gwamnati ta yi garambawul ga tsarin tsaro na Nijeriya.
Kungiyar, ta ce karin kudin man fetur da harajin kayayyaki zai kara radadin talaucin da ake fama da shi a Nijeriya.
Shugaban kungiyar Kwadago na kasa Ayuba Wabba da shugaban Kungiyoyin ‘yan kasuwa Bobboi Bala Kaigama su ka bayyana haka yayin wani taro da su ka yi a Abuja.
Ayuba Wabba, ya ce su na juyayin yadda ake samun layin ababen hawa a gidajen mai, wanda sun yi imani hakan ya faru ne saboda shawarar da asusun bada lamuni na duniya ya ba gwamnati cewa ta janye tallafin man fetur.
Ya ce abinda asusun ke nufi da janye tallafin man fetur shi ne karin kudin man fetur da karin walhalun rayuwa.