Dan majalisar wakilai daga jihar Neja Abubakar Chika Adamu, ya ce sama da shekara daya kenan ba ya iya zuwa kauyen su balle ya kwana sakamakon yawaitar hare-haren yan bindiga.
Chika ya bayyana haka ne yayin zaman majalisar na ranar Alhamis da ta gabata, inda ya koka a kan matsanancin rashin tsaro da jama’ar sa ke fama da shi.
Haka kuma, wasu ‘yan majalisa sun bayyana koken su game da tabarbarewar tsaro da ya addabi yankin, tun daga matsalar garkuwa da mutane, da harin ‘yan bindiga, da rikicin Fulani da makiyaya da sauran su.
Dan majalisa daga karamar hukumar Safana ta jihar Katsina Ahmad Dayyabu Safana, ya ce hare-haren da ake kaiwa a mazabar shi sun kazanta, duba da yadda mahara ke kashe mutane babu kakkautawa tare da kona gidajen su sannan su yi awon gaba da wasu. Bayan sauraren korafen-korafen ‘yan majalisun ne, majalisar ta yanke shawarar gayyatar shugaba Muhammadu Buhari ya gurfana a gabanta domin tsatsatsage mata bayani game da kokarin da ya ke yi na shawo kan matsalar.