Home Labaru Siyasar Edo: Rikici Na Kara Tsamari Tsakanin Oshiomhole Da Gwamna Obaseki

Siyasar Edo: Rikici Na Kara Tsamari Tsakanin Oshiomhole Da Gwamna Obaseki

316
0

Rikicin siyasa a tsakanin Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole da gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki na kara ta’azzara.

Yanzu haka gwamna Obaseki ya dakatar da kwamishinoni takwas daga majalisar zartarwa ta jihar, wadanda sun kasance na hannun damar Adams Oshiomhole.

Kwamishinonin da lamarin ya shafa kuwa sun hada da na makamashi da ruwa Joseph Ugheoke, da kwamishiniyar harkokin mata da ci-gaban jama’a Magdalene Ohenhen, da kuma kwamishinan wadata kayayyakin aiki Osahon Amiolemen.

Sauaran sun hada da kwamishinan lafiya David Osifo, na matasa da ayyukan musamman Mike Amanokha, da kwamishiniyar kasafi Mariam Abubakar, da na ayyuka Emmanuel Usoh da kuma na kimiya da fasaha Chrisopher Adesotu.

Leave a Reply