Home Labaru Buhari Ya Kalubalanci Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki Ta Kara Himma

Buhari Ya Kalubalanci Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki Ta Kara Himma

220
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shughaban kasa Muhammadu Buhari, ya yarda da cewa gwamnatin sa ba ta yi hobbasa a bangaren samar da wutar lantarki ba, ya na mai cewa akwai bukatar kamfanonin rarraba wutar su kara himma.

Buhari ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya za ta yi iyakar kokarin ta wajen ganin an inganta samar da wutar lantarki a Nijeriya.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne, yayin wata ganawa da ya yi da majalisar sarakunan gargajiya na jihar Edo bisa jagorancin Oba na Benin Omo N’oba N’ Ewuare II, a fadar sa da ke Abuja.

Oba na Benin, ya roki shugaba Buhari ya taimaka wajen ganin an magance matsalar rashin wutar lantarki a jihar Edo, ya na mai bayyana matsalar a matsayin abin takaici.

Da ya ke amsa bukatar Sarkin, shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Nijeriya su kwantar da hankulan su, ya na mai yin kira da a kara hakuri da kamfanonin rarraba wutar lantarkin.

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Femi Adesina, ya ce shugaba Buhari ya ce gwamnatin sa ta yi kokari wajen inganta wutar lantarki a baya, amma akwai bukatar a kara himma.

Leave a Reply