Babbar kotun tarayya da ke a Kano, ta bada umurnin a sauya hanyar isar da sammaci ga hukumar EFCC, dangane da karar da wani lauya Barista Audu Bulama Bukarti ya shigar, inda ya bukaci EFCC ta bayyana rahoton binciken da kwarraru su ka gudanar a kan bidiyon gwamna Ganduje na karbar daloli.
Lauya Bulama dai ya na tuhumar EFCC a kan kin bayyana ma shi rahoton binciken da ta gudanar a kan bidiyon da ke nuna gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya na karbar cin hanci daga ‘yan kwangila.
A cewar lauyan, kin bayyana rahoton binciken kamar tauye ma shi hakkin ne na sanin duk bayanan da dokar ‘yancin sanin bayanai ta shekara ta 2011 ta tanada.
Da ya ke zartar da hukunci a kan lamarin, Mai shari’a Obiora Egwuata ya bada umurnin a sauya hanyar isar wa hukumar EFCC sammaci da sauran takardun shigar da kara ta hanyar lika takardun a ofishin ta da ke karamar hukumar Fagge a jihar Kano.
Alkalin ya kara da cewa, a maido wa kotu shaidar hoton da ke nuna an lika takardar sammacin a ofishin EFCC kamar yadda ya umurta, inda daga bisani ya dage sauraren karar zuwa ranar 8 ga watan Oktoba.