Home Labaru Siyasar Aljeriya: Bouteflika Ya Sauka Daga Mukamin Sa Na Kujerar Shugaban Kasar

Siyasar Aljeriya: Bouteflika Ya Sauka Daga Mukamin Sa Na Kujerar Shugaban Kasar

358
0

Hukumomin kasar Aljeriya sun bada sanarwar yin murabus din
shugaban kasar Abdul’aziz Bouteflika wanda ya sha fama da
rashin lafiya tsawan lokaci.
Sanarwar hakan na zuwa ne bayan shafe tsawon mako guda ana
gudanar dazanga-zangar nuna kin amincewa da matakin
shugaban kasar da gwamnatin sa.
Ofishin Shugaban kasar ya ce, Shugaba Bouteflika, zai sauka
zuwa ranar 28 ga watan Afirilu, lokacin da wa’adinsa zai cika.
Kamfanin Dillancin Labaran gwamnatin Kasar ta APS, ya yada
labaran tun jiya.
Kafar ta APS, ta ce Shugaba Boutrflika zai tabbatar da ci gaba
da dorewar cibiyoyin gwamnati kafin ya sauka.
Wannan sanarwar na zuwa ne bayan shafe tsawon mako guda da
aka yi ana ta zanga-zangar nuna bijirewa ga Shugaban Kasar da
gwamnatinsa.
A makon jiya, Hafsan Hafsoshin sojojin Algeria mai karfin fada
a ji, ya girgiza kasar bayan da ya yi kiran da a ayyana Shugaba
Bouteflika a matsayin mara sukunin iya shugabantar Kasar, a
kuma saukar da shi.
Fadar gwamnatin Algeria ta ce Shugaban Kasar AbdelAziz
Bouteflika zai yi murabus kafin ranar 28 ga watan Afrilu,
lokacin da wa’adinsa zai kare.
Matakin amincewa da yin murabus din Bouteflika, ya zo ne
bayan da manyan jam’iyyun siyasar Kasar ciki har da tasa, suka
goyi bayan dubban ‘yan Kasar da ke zanga-zangar neman tilasta
masa sauka daga mulki.
Cikin sanarwar da ta fitar a yau Litinin, fadar Gwamnatin ta
Algeria ta ce Shugaba Bouteflika mai shekaru 82 zai sauka ne
bayan daukar wasu muhimman matakai, wadanda ba a bayyana
ba.
Matsin lambar tilastawa Bouteflika yin murabus ya soma ne
bayan da Shugaban ya bayyana aniyar neman wa’adi na 5 a
babban zaben Kasar da a baya aka tsara zai gudana a ranar 18 ga
watan Afrilu.
Bayan zazzafar zanga-zangar dubban ‘yan Algeria, Bouteflika
ya janye aniyarsa ta neman tazarce, amma da sharadin dage
zabukan Kasar zuwa wani lokaci da bai bayyana ba.
Matakin Shugaban na Algeria ya sake tunzara masu zanga-
zangar wadda dubban dalibai da malamansu da kuma manyan
lauyoyi suka shiga.

Leave a Reply