Hukumar Zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce za ta saurari sakamakon hukuncin kotun koli ta Nijeriya, kafin daukar mataki na gaba a kan zaben fidda gwanin jam’iyyar APC a jihar Zamfara.
Hukumar ta bayyana matsayin ta ne, bayan matakin da ta dauka na kin ba dan takarar APC Muhktar Shehu takardar shaidar nasarar lashe zaben kujerar Gwamnan jihar.
A cewar hukumar, ta dauki matakin ne saboda hukuncin kotun daukaka kara da ke jihar Sokoto na soke zaben fidda gwanin jam’iyyar APC.
Tuni dai APC ta maida martani a kan matakin hukumar zabe, inda ta musanta cewa hukuncin kotun daukaka kara ya soke zaben fidda gwanin da ta yi, don haka ta gaggauta mika wa dan takarar ta shaidar sa ta lashe zaben kujerar gwamnan jihar Zamfara. Sai dai hukumar zaben ta hannun kwamishinan ta na kasa kan wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye, ta sha alwashin bin doka da umarnin kotu a kan wannan takaddama, ta na mai cewa ba ta da wani dan takara da ta fifita a jihar Zamfara, kawai ta damu ne da bin tsarin da doka ta shimfida.
You must log in to post a comment.