Home Labaru Rashin Takardu: Kotu Ta Yi Watsi Da Takarar Sanata Adeleke Na Jam’iyyar...

Rashin Takardu: Kotu Ta Yi Watsi Da Takarar Sanata Adeleke Na Jam’iyyar PDP

317
0

Mai shari’a Usman Musa na babbar kotun Bwari da ke Abuja ya
yi watsi da zaben Sanata Ademola Adeleke a matsayin dan
takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Osun da aka
gudanar a watan Satumbar shekara ta 2018.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC biyu suka maka Adeleke gaban
kotu, inda suka zarge shi da gazawa wajen mallakar sahihan
takardun kammala makarantar sakandire, wanda a cewar su bai
cancanta ya tsaya takarar gwamna ba.
Da ya ke yanke hukunci a ranar Talatar da ta gabata, mai shari’a
Usman Musa, ya soke zaben Adeleke a matsayin dan takarar
jam’iyyar PDP, kasancewar ya karya dokar sashe na 177 da ke
cikin kundin dokar kasa na shekara ta 1999 da aka yi wa
kwaskwarima.
Sashen ya ce wajibi ne dan takarar kujerar gwamna ya mallaki
matakin karatu har zuwa sakandire, saboda haka mai shari’a
Musa ya ce bayanan da kotu ta tattara sun nuna cewa Adeleke ya
shiga makarantar sakandire ne a shekara ta 1976, kuma babu
wani bayani da ya nuna cewa ya kammala karatun, kasancewar
babu sunan sa a cikin kundin daliban makarantar tun daga 1980.

Leave a Reply