Home Labaru Shugabancin Majalisa: Dalilin Goyon Bayan Sanata Lawan Da Gbajabiamila – Tinubu

Shugabancin Majalisa: Dalilin Goyon Bayan Sanata Lawan Da Gbajabiamila – Tinubu

185
0

Jagoran jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya karyata jita-jitar cewa ya na goyon bayan Sanata Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila ne domin share wa kan sa hanyar zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a shekara ta 2023.

Tinubu ya ce ya na goyon bayan a zabi Lawan da Gbajabiamila ne saboda su mara wa Shugaba Muhammadu Buhari baya, musamman a kan yadda zai samu nasarar gudanar da mulki a zangon sa na biyu.

Ya ce an yi kuskure a shekara ta 2015, inda aka yi sakaci har Sanata Saraki da Yakubu Dogara su ka zama shugabannin majalisun tarayya, inda su ka shafe shekaru hudu su na rike kasafin kudi tare da kawo tsaiko a kan muhimman ayyukan raya kasa da Shugaba Buhari ya sha alwashin sama wa ’yan Nijeriya.

Bola Tinubu, ya ce kwata-kwata ba gaskiya ba ne a ce ya na azarbabin neman takarar shugabancin Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun sa Tunde Rahman ya fitar, Tinubu ya ce irin yadda akidar siyasar shi ta sa gaba, ta zama shaida a gare shi cewa shi ba mutum ba ne mai kwadayin mulki.