Home Labaru Zargin Kashe Farar Hula: Sarakunan Zamfara Sun Nemi Yafiyar Sojin Saman Nijeriya

Zargin Kashe Farar Hula: Sarakunan Zamfara Sun Nemi Yafiyar Sojin Saman Nijeriya

403
0

Sarakunan Jihar Zamfara sun nemi gafarar rundunar sojin sama ta Nijeriya, biyo bayan zargin da su ka yi mata na kashe fararen hula da gangan a hare-haren da ta kai domin kakkabe ‘yan bindigar da su ka hana zaman lafiya a Jihar.

Shugaban Majalisar Sarakuna kuma Sarkin Zamfaran Anka Attahiru Ahmed, ya gabatar da neman gafarar ne lokacin da tawagar binciken lamarin da gwamnati ta kafa ya ziyarci garin Anka a karshen makon da ya gabata.

Basaraken, wanda ya bayyana takaicin sa a kan matsalar da zargin ya haifar, ya bukaci sojojin su rika kiyayewa wajen tantance ‘yan ta’adda da fararen hula a lokacin kai hari.

Shugaban tawagar binciken Idi Lubo, ya ce sun je Zamfara ne domin tantance abin da ya faru da kuma neman gafara a kan matsalar da aka samu.

Leave a Reply