Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta fara gudanar da bincike a game da wasu kudi da ake zargin sun bace a hukumar shirya jarabawa share fagen shiga jami’a ta JAMB daga shekara ta 2010 zuwa 2016.
EFCC dai ta na kokarin gano yadda aka rika tafka sata a hukumar JAMB kamar yadda rahotanni su ka bayyana.
Rahotanni sun nuna cewa, hukumar EFCC za ta dira kan jami’an hukumar JAMB 15 da ake zargi da aikata ba daidai ba.
Idan dai ba a manta ba, a shekara ta 2018, wata Philomena Chieshe ta yi ikirarin cewa maciji ya hadiye kudi naira Miliyan 36 na hukumar JAMB.
Bincike ya nuna cewa, Naira Biliyan 8 da miliyan 7 da hukumar ta ke tarawa a baya, ya kan kare ne a cikin aljihun wasu tsirarrun manyan ma’aikata, inda jami’an hukumar ke bada uzuri da hadarin mota ko gobara ko kuma rikicin Boko Haram.