Home Labaru Shugabancin CBN: Majalisa Ta Fara Shirin Tabbatar Da Godwin Emeifele

Shugabancin CBN: Majalisa Ta Fara Shirin Tabbatar Da Godwin Emeifele

304
0
Majalisar Dattawa

Majalisar dattawa ta fara daukar matakan tabbatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan bankin Nijeriya CBN karo na biyu.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, ya karbi wasikar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika ta neman tabbatar da sabunta nadin Godwin Emefiele a makon da ya gabata.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Sanata Bukola Saraki ya karanta wasikar da shugaba Buhari ya aike a zauren majalisar ranar Alhamis da ta gabata.

Tuni dai majalisar ta mika wasikar ga kwamitin harkokin banki da inshora domin daukar matakan da su ka dace.

Yanzu haka dai kallo ya koma a kan majalisar, don ganin hanyar da za ta bi a kan binciken zargin da ake yi wa Emefiele kafin ta tabbatar da shi. Wasu dai na ganin ziyarar da Emefiele ya kai wa shugaba Buhari, ba ta rasa nasaba da zargin da ake yi masa na yin sama da fadi da kimanin naira biliyan 500 ba, inda wasu ke tunanin Emefiele ya ziyarci Buhari ne domin ya wanke kan sa daga zargin badakalar.