Home Labaru Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Ce Ba Su Ba Kungiyar Miyetti Allah...

Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Ce Ba Su Ba Kungiyar Miyetti Allah Ko Kwabo Ba

280
0
Gwamnatin Tarayya

Ministan harkokin cikin gida Janar Abdulrahman Danbazau, ya ce gwamnatin Tarayya ba ta ba kungiyar Fulani ta Miyetti Allah kudi ba yayin tattaunawar ta da su a Birnin Kebbi.

Dambazau ya bayyana haka ne, yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a garin Anka na jihar Zamfara, inda shaida wa sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmad cewa ya je ne a madadin shugaba Muhammadu Buhari domin tattaunawa a kan matsalar rashin tsaro a jihar Zamfara.

Janar Dambazau ya kuma ba manoma tabbacin cewa, gwamnati za ta sama masu isasshen tsaro a lokutan ayyukan noma da kuma rani.

Sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmad Ahmad, ya ce ba za a gudanar da ayyukan noma a jihar ba har sai an dauki mataki mai tsanani, ya na mai cewa yawancin al’umma sun yi gudun hijira daga kauyukan su, kuma mafi yawancin mata da yara sun koma da zama a birane.Ya ce a wannan lokacin, akwai sama da mutane 16,000 da su ka balle daga asalin su bayan sun kubuta daga hare-haren ‘yan bindiga a kayyuka.

Leave a Reply