Home Labaru Wata Sabuwa: An Bukaci Kotun Zabe Ta Dakatar Da Rantsar Da Shugaba...

Wata Sabuwa: An Bukaci Kotun Zabe Ta Dakatar Da Rantsar Da Shugaba Buhari

647
0

Jam’iyyar Hope Democratic Party HDP, ta shigar da wata kara da ke neman kotun sauraren kararrakin zaben Shugaban kasa ta bada umurnin dakatar da rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayu.

Haka kuma, Jam’iyyar ta bukaci a hana rantsar da Shugaban alkalan Nijeriya a ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 2019.

A wani jawabi da manema labarai suka samu a ranar Talata, 14 ga watan Mayu, ta shigar da kara akan dalilai shida daidai da sashi daya ayan na biyu a kundin tsarin mulkin 1999.

Wasu daga cikin dalilan jam’iyyar na shigar da karar su ne, cewa akwai wata shari’a a kasa da ke kalubalantar nasarar shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shekara ta 2019.Jam’iyyar ta kara da cewa, duk da shari’ar da ake yi da Shugaba Muhammadu Buhari, amma ana ta kokari da shirye-shiryen rantsar da shi da Shugaban alkalan Nijeriya a ranar 29 ga watan Mayu.

Leave a Reply