Home Labaru Shawara: Dole PDP Ta Kakkabe Bara-Gurbi Domin Dawo Da Kimar Ta –...

Shawara: Dole PDP Ta Kakkabe Bara-Gurbi Domin Dawo Da Kimar Ta – Obasanjo

351
0
Olusegun Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasa
Olusegun Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasa

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce ya zama wajibi jam’iyyar PDP ta kakkabe baragurbin da ke cikin ta kafin ta maido da martabar ta a idon mutane.

Obasanjo, ya kuma bukaci shugabannin jam’iyyar PDP su yi zawarcin mutanen da ya kira masu mahimmanci, wadanda  za su bada gudunmuwa duk wuya duk runtsi.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne, yayin da tawagar shugabannin PDP daga yankin Kudu maso Yammacin Nijeriya ta ziyarce shi a gidan sa da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun.Ya ce da dama daga cikin shugabannin PDP su na cika aljihun su da tumbin su ne kawai, ya na mai cewa gurbatattun ‘ya’yan jam’iyyar ba su da jajircewar maido da martabar da ta rasa.

Leave a Reply