‘Yan majalisar dattawa sun yi alkawarin kammala duk aikin da ya dace a kan kasafin bana nan da makonni biyu masu zuwa.
Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, ya ce za su yi kokari su karasa aikin kasafin kwanan nan, ya na mai cewa za a karkare aikin ne a ranar 16 ga Watan Afrilu.
Bukola Saraki, ya yi kira ga kwamitin da ke aiki a kan kasafin su gaggauta kammala aikin su a ranar Juma’a mai zuwa, sannan su gabatar wa majalisa duk aikin da su ka yi nan da mako guda.
Yanzu haka dai an dage zaman majalisar zuwa ranar 9 ga watan Afrilu, domin a ba shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya damar gabatar da kasafin su na shekara shekara ta 2019.