Home Labaru Kiwon Lafiya Kiwon Lafiya: Dole Asibitin Fadar Shugaban Kasa Ya Yi Aikin Da Aka...

Kiwon Lafiya: Dole Asibitin Fadar Shugaban Kasa Ya Yi Aikin Da Aka Dora Ma Shi – Buhari

512
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bada umarnin a gaggauta maida asibitin Fadar Shugaban Kasa ya rika gudanar da ainihin aikin da aka kafa shi don shi.

Kamar yadda wani babban jami’i a fadar shugaban kasa ya bayyana, ya ce tun farko an gina asibitin ne domin kula da lafiyar iyalan Shugaban Kasa da na Mataimakin sa da ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Babban Sakatare na Fadar Shugaban Kasa Jalal Arabi ya bayyana haka, yayin da ya bayyana a gaban Kwamitin kasafi na Majalisar Dattawa.

Arabi ya kara da cewa, tunanin hana kowa zuwa asibitin sai iyalan Shugaban Kasa da na Mataimakin sa da ma’aikatan gidan gwamnatin ya fito ne daga Ofishin Shugaban Kasa shi kan sa.Ya ce an yi haka ne, domin a tabbatar da asibitin ya na aikin da ya kamata ta yadda wadanda aka gina shi domin su za su rika cin moriyar sa.

Leave a Reply