Home Labaru Shari’ar Zabe: Ba Mu Tura Sakamakon Zabe A Yanar Gizo Ba –...

Shari’ar Zabe: Ba Mu Tura Sakamakon Zabe A Yanar Gizo Ba – Shugaban INEC

365
0
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta kasa, INEC

Shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana dalilin da ya hana hukumar tura sakamakon zabe a yanar gizo, sabanin abin da jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar ke ikirari.

Jawabin dai ya bayyana ne a gaban kotun sauraren kararrakin zabe a Abuja, inda lauyan shugaba Buhari Alex Izinyon ya kunna wani faifan bidiyo da ke nuna shugaban hukumar zabe ya na bayani a kan dalilin da ya hana hukumar amfani da yanar gizo.

A cikin faifan bidiyon, Farfesa Mahmoud ya yi bayanin cewa, hukumar ta gaza yin amfani da yanar gizo wajen tattara sakamakon zaben ne saboda karancin na’urorin sadarwa da tsoron ‘yan damfarar yanar gizo.

Haka kuma, lauyan ya gabatar da wani bidiyo na daban, wanda ke dauke da hirar Farfesa Mahmoud Yakubu da wani dan jarida, inda ya yi bayani a kan kalubalen da ke tattare da tura sakamakon zabe a yanar gizo.

Leave a Reply