Home Labaru Gyara-Kayan-Ka Tsokacin Masana A Kan Sabuwar Wasikar Obasanjo

Gyara-Kayan-Ka Tsokacin Masana A Kan Sabuwar Wasikar Obasanjo

171
0
Olusegun Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasa
Olusegun Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasa

Kalubalen da Nijeriya ke fuskanta daga bangarori daban-daban na ci-gaba da haifar da muhawara akan gazawa da kuma kokarin hukumomi wajen kawo karshen matsalolin da ke ci wa jama’a tuwo a kwarya musamman sha’anin tsaro.

Wasu bangarori dai su na kallon matsalar tsaro a matsayin gazawar gwamnatin shugaba Buhari, kamar yadda Farfesa Wole Soyinka ya bayyana yayin da ya ke tsokaci a kan halin da tsaro ke ciki.

Haka kuma, Janar Olusegun Obasanjo ya rubuta wa shugaba Buhari budaddiyar wasika, inda ya gargade shi ya gaggauta daukar matakan ceto Nijeriya, wadda a yanzu ta kama hanyar tabarbarewa saboda matsalolin tsaro da ke haifar da rasa dimbin rayuka.

‘Yan Nijeriya dai na ci-gaba da muhawara a kan wasikar Obasanjo, inda wasu ke goyon bayan abubuwan da ya zayyana a ciki, tare da bukatar ganin an saurare su da kunnen basira, yayin da a gefe guda wasu ke kallon wasikar a matsayin yunkurin haifar da ce-ce-ku-ce. �AC����,�