Home Labaru Tsaro Boko Haram: Muna Ci-Gaba Da Tattaunawa A Kan Sauran ‘Yan Matan Chibok...

Boko Haram: Muna Ci-Gaba Da Tattaunawa A Kan Sauran ‘Yan Matan Chibok – Garba Shehu

225
0
Garba Shehu, Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasa
Garba Shehu, Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasa

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu, ya ce gwamantin shugaba Muhammadu Buhari na ci-gaba da tattaunawa da kungiyar Boko Haram a kan yadda za a sama wa ragowar ‘yan matan Chibok ‘yanci.

Kungiyar Boko Haram dai ta yi awon gaba da dalibai mata 276 daga makarantar su da ke Chibok a jihar Borno, sai dai gwamnatin tarayya ta yi nasarar ceto wasu daga cikin su.

Wata tsohuwar ma’aikaciyar gidan talabijin na CNN Issha Sesay, ta fadi a cikin slittafin da ta wallafa cewa an manta da sauran ‘yan matan da ke tsare saboda sun fito daga gidan talakawa.

Yayin da ya ke maida martani, Garba Shehu ya ce abubuwan da aka fadi ba gaskiya ba ne, ya na mai cewa kuskure ne a ce gwamnati ta rasa wanda za ta tunkara domin ceto sauran ‘yan matan. A karshe ya ce kuskure ne a rika sukar gwamnatin shugaba Buhari bisa barambaramar da gwamatin Jonathan ta yi a baya.