Home Labaru Sarauta: Kotu Ta Dakatar Da Shirin Gwamnatin Kano Na Karin Masarautu 4

Sarauta: Kotu Ta Dakatar Da Shirin Gwamnatin Kano Na Karin Masarautu 4

506
0

Wata babbar kotu da ke Ungoggo, a jihar Kano ta bada umarnin dakatar da shirin Gwamnatin jihar, na karin masarautu 4, zuwa masu daraja ta 1 a Jihar.

Kafin umarnin kotun dai a yau Asabar ne gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, ke shirin bikin nadin sabbin Sarakunan 4 a masarautun da suka hada da Rano, Bichi, Gaya da kuma Karaye.

Yayin zaman shari’ar a ranar Juma’ar nan, mai shari’a Nasiru Saminu, da ya yanke hukuncin ya kuma bada umarnin dakatar da buga takardun da ke bayyana dokar da ta bada damar daga darajar Karin masarautun guda 4.Alkalin ya tsayar da 15 ga watan Mayu da muke ciki a matsayin ranar da zai ci gaba da sauraron shari’ar

Leave a Reply