Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar dinkin duniya ya tabbatar da sako wasu kananan yara kimanin 900 da Jami’an tsaron sa kai a Najeriya suka yi amfani da su tsawon lokaci a yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabas.
Sanarwar da asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta fitar a ta nuna cewa, bayan sakin yaran su 900 a makon nan hakan ya mayar da adadin da jami’an sa kan suka saki zuwa dubu 1 da 700.
Adadin dai a cewar sanarwar ta UNICEF wani bangare ne na adadin yara fiye da dubu 3 da dari 5 da Jami’an tsaron sa kai a Najeriyar suka dauka aiki tsakan-kanin shekarun 2013 zuwa 2017 don yaki da mayakan kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.
A cewar shugaban asusun na UNICEF, matakin, yunkuri ne mai kyau na ci gaba da kare hakkin kananan yara a Najeriyar, musamman yankin arewa maso gabas, da ke fuskantar yaki tsawon shekaru, Mohamed Fall, ya ce dole ne a jinjinawa jami’an tsaron sa kan, wadanda e aiki kafada-da-kafada da dakarun sojin kasar a yaki da Boko Haram.Tun a shekarar 2017 ne kungiyar tsaron sa kan a Najeriya, ta kawo karshen matakin amfani da kananan yaran a yaki da boko haram inda nan take ta saki kananan yara 833.