Home Labaru Dambarwa: Kirkirar Sabbin Masarautu Ba Zai Karya Lagon Masarutar Kano Ba –...

Dambarwa: Kirkirar Sabbin Masarautu Ba Zai Karya Lagon Masarutar Kano Ba – Isa Sunusi

733
0

Tsohon sakataren sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu Isa Sanusi ya ce rarraba masarautu da aka yi ba zai taba karya lagon masarautar jihar ba.

Sunusi ya bayyana haka ne bayan gurfana da ya yi a ofishin hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano don amsa wasu tambayoyi kan zargin facaka da kudaden masarautar.

Hukumar ta gayyaci shi ne tare da dan Buran din Kano Munir Sunusi, wanda shi ne shugaban ma’aikatan fadar sarkin, da akantan masarautar da kuma Falakin Kano Mujitaba.

An dai gayyaci wadannan mutane ne domin su yi bayanin kan zargin kashe kudaden masarautar ba bisa ka’ida ba.

A baya dai hukumar ta dakatar da wannan bincike, sai dai an sake waiwayensa a wannan karon.

Bincike na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Kano ta fara wani yunkuri na kirkiro karin masarautu, abin da wasu ke ganin hakan yunkuri ne na rage wa Sarki Sanusi karfin iko.

Bayan fitowarsa daga wajen binciken tsohon sakataren Isa Sanusi, wanda aka sauke saboda zargin zagon kasa, ya ce yana goyon bayan binciken da ake yi.

Leave a Reply