Home Labaru Samar Da Ruwa: Gwamnatin Katsina Ta Ce Tsaffin Injina Ke Haifar Da...

Samar Da Ruwa: Gwamnatin Katsina Ta Ce Tsaffin Injina Ke Haifar Da Karancin Ruwa

385
0

Hukumar samar da ruwan sha ta jihar Katsina ta ce matsalar
karancin ruwan sha da ake fama da shi babban birnin jihar bai
rasa nasaba da tsaffin injinan tura ruwan da ake amfani sa su.
Babban daraktan hukumar Babangida Abubakar ne ya bayyana
haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Katsina.
Abubakar ya ce, daga yanzu za a ci-gaba da samun tsaftatacce
kuma wadataccen ruwan shan a duk wuraren da matsalar ta
shafa da zaran an kamala sa sabbin injunan tura ruwan a Dam
din Ajiwa da ke jihar.
Daraktan ya kara da cewa, kimanin shekaru 10 kenan aka sanya
wasu injunan tura ruwa da ke bada matsala wajen tafiyar da aiki
yadda ya kamata, kuma ko an gyara su ba su wuce kwanaki biyu
ko uku sai su kara lalacewa, domin ba su iya samar da ruwan da
ake bukata a birnin wanda ke samun karuwar al’umma a koda
yaushe.
Babangida Abubakar ya bukaci daukacin al’ummar yakin da
matsalar ta shafa su kara hakuri, domin gwamnati ta dauki
matakan da suka dace don magance matsalar.

A karshe ya ce gwamnati ta gina tashoshin turo ruwan a wasu
wurare na musamman, domin tabbatar da samar da ruwan a
wuraren da ake fama da karancin sa.

Leave a Reply