Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Sojojin Sama Sun Tarwatsa Sansanin Boko Haram A Jihar...

Yaki Da Ta’addanci: Sojojin Sama Sun Tarwatsa Sansanin Boko Haram A Jihar Borno

1089
0

Rundunar sojojin sama ta Nijeriya ta ce ta samu nasarar kai
samame a mafakar ‘yan kungiyar Boko Haram da suka yi
muba’yi’a da bangaren masu ikirarin jahadi ISWAP a arewacin
jihar Borno.
Daraktan yada labarai na rundunar Ibikunle Daramola ya
bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya rabawa manema
labarai a ranar Talatar da ta gabata, jim kadan bayan wani
samamen hadin gwiwa da ta kai a mafakar mayakan, ranar
Litinin.
Daramola ya kara da cewa, sojojin sun samu nasarar halaka
wasu daga cikin shugabanin kungiyar ta ISWAP tare da
mayakan ta a kauyen Magari da ke zirin Tafkin Chadi jihar
Borno.
Haka kuma Daramola ya yi karin hasken a kan cewa, sun kai
samamen ne baya sun samu wasu bayanan sirri da ke tabbatar
musu da cewa, kwamandojin kungiyar sun tattaru a yankin tare
da sauran mayakan su.
Daramola ya ce bama-bamai da muka cilla daga jiragen yaki sun
dira ne a dai-dai wajen da suka saita su, inda riransu ka da waya
sai suka tarwatse, wanda hakan ya jawo mutuwar ‘yan kungiyar
da dama.

Leave a Reply