Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari hannun ka mai sanda game da abubuwan da ke faruwa a Nijeriya.
A hira da ya yi da kafar yada labarai ta BBC, Bafarawa ya bayyana rashin tsaro a matsayin babbar matsalar da Nijeriya ke fuskanta, inda ya bayyana matsalar garkuwa da mutane a matsayin abin da ya ki ci ya ki cinyewa.
Ya ce bai ga wani ci-gaba da aka samu ba a Nijeriya, ya na mai cewa gara ma gwamnatin baya a kan ta yanzu.
Bafarawa ya kara da cewa, bai taba jin shugaba Buhari ya zauna da gwamnonin Arewa domin tattauna matsaloli da mafitar arewa ba.