Home Labaru Sadaukar Da Kai: Zan Bada Gudummawa Wajen Cigaban Nijeriya Idan Na Samu...

Sadaukar Da Kai: Zan Bada Gudummawa Wajen Cigaban Nijeriya Idan Na Samu Dama – Baru

383
0

Babban manajan daraktan kamfanin NNPC mai barin gado  Maikanti Baru, ya ce a shirye ya ke sadaukar da kan sa don cigaban Nijeriya  idan an sake bashi dama.

Mai kanti Baru ya bayyana haka ne a lokacin  da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron karramawa da kungiyar injiniyoyi ta gudanar a jihar Lagas.

Da ya ke magana a kan shirye shiryen sa na yin ritaya daga aiki a ranar 7 ga wata Yuli, Baru ya ce a shirye ya ke domin yi wa Nijeriya hidima muddin ya sake samun damar yin hakan.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ta rahoto cewa, Mai kanti Baru zai cika shekaru 60 da haihuwa wandahakan ya sa dole ya ajiye aiki a ranar7 ga watan Yuli.

An dai haifi Baru ne a ranar 7 ga watan Yulin shekara ta 1959 ya kuma kasance dan jihar Bauchi, amman ya yi rayuwar sa a jihar Plateau, kuma ya halarci jami’ar Ahmadu Bello Zaria, inda ya kammala karatun digirin sa na farko a fannin injiniya, daga bisani ya kuma yi digirin sa na uku a fannin injiniya.Idan dai ba a manta ba, a ranar Alhamis din da ta gabata ne  shugaban kasa Buhari ya sanar da nadin Mele Kolo Kyari a matsayin sabon shugaban kamfanin NNPC.

Leave a Reply