Home Labaru Damfara: EFCC Ta Gurfanar Da Wani Ba-Amurke Da Ya Yaudari ‘Yan Nijeriya...

Damfara: EFCC Ta Gurfanar Da Wani Ba-Amurke Da Ya Yaudari ‘Yan Nijeriya Daloli

314
0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta sake gurfanar da wani dan kasar Amurka mai suna Marco Ramirez bisa tuhumar sa da damfarar wasu ‘yan Najeriya uku dala miliyan 1 da dubu dari 2.

Ramirez ya damfari mutanen ne bisa yaudarar su a kan cewa, zai samar musu shaidar zama ‘yan kasar Amurka.

An sake gurfanar da Ramirez a gaban kotun ne bisa tuhumar sa da laifuka 12 da suka hada da karya da damfara da yaudara da kuma  zamba cikin aminci.

Hukumar EFCC ta ce Ramirez ya aikata laifukan  ne a tsakanin watan Fabarairu da Agusta na shekara ta 2013 a jihar Legas, sannan mutanen da Ramirez ya damafara sun hada da Godson Echejue da Abubakar Umar da Olukayode Sodimu.

Laifukan da Ba-Amurken ya aikata, sun sabawa sashe na 1(3) na kundin aikata manyan laifukan da suka shafi damfara da laifuka masu alaka da hakan wanda aka kirkira a shekara ta 2006.

Leave a Reply