Kungiyar gwamnonin Nijeriya NGF ta gudanar da wani taro a Abuja, domin tattaunawa a kan wasu abubuwa da suka shafi harkokin kasa ta fannin samar da kudaden shiga da kuma inganta tsaro.
Taron wanda ya gudana a babban ofishin kungiyar da ke Maitama Abuja, ya maida hankali ne a kan sharhin ganawar gwamnoni da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan harkokin tsaro.
Haka kuma ganawar ta gudana ne da nufin ta tabbatar da shirin gwamnonin na mu’amala da babban bankin duniya domin inganta hanyoyin samar da kudaden shiga a jihohin Nijeriya.
Gwamnonin sun kuma tattauna a kan tsare-tsaren da hukumar yaki da cin hanci da rashawa a sirrance ta shimfida wajen tabbatar da kananan hukumomin Nijeriya sun fara cin gashin kan su a duk wata.
Gwamnonin da suka halarci zaman taron sun hada da na jihohin Ekiti da da Sokoto da Osun da Ondo da Borno da Ogun, da Legas da Edo da Oyo da kuma na Ebonyi.Sauran gwamnonin sun hada na Kano da Gombe da Kebbi, da Filato da Kaduna da Bayelsa da Nasarawa da Neja da da Jigawa.