Home Labaru Sabon Tsarin Albashi: Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Kwamitin Samar Da Mafita

Sabon Tsarin Albashi: Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Kwamitin Samar Da Mafita

1701
0
Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamiti mai mutane 22 tare da bas hi wata guda ya tabbatar an biya ma’aikata sabon tsarin biyan albashi.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya kaddamar da kwamitin, wanda shugaban ma’aikata Winfred Oyo-Ita zai jagoranta.

Wasu daga cikin ‘yan kwamitin sun hada da ministan kwadago da ministan kasafin kudi da ministan lafiya  da kuma babban lauyan Nijeriya.

A lokacin da ya ke zantawa da kwamitin, sakataren gwamnatin tarayya ya bayyana cewa, aikin kwamitin shine ya dai-dai-ta tsarin biyan albashin ma’aikata sakamakon gyara mafi karancin albashi da aka yi.

Oyo-Ita ya ce duba da yanayin da ake ciki na tattalin arzikin kasa, kwamitin zai yi aiki bil hakki don ganin an samu sakamako mai kyau.