Home Labaru Zaben Kaduna: Shedun Da PDP Ta Gabatar Sun Ce Ba A Yi...

Zaben Kaduna: Shedun Da PDP Ta Gabatar Sun Ce Ba A Yi Zabe A Wasu Yankuna Ba

628
0

A cigaba da gudanar da shari’ar zaben shekara ta 2019, Jam’iyyar PDP ta gabatar da wasu daga cikin shaidun ta a gaban kotun da ke sauraran kararrakin zabe a jihar Kaduna.

Wani daga cikin wadaada suka bada shaida a gaban kotun ya ce, yi zaben gwamnan jihar Kaduna ne cikin hatsaniya ba tare da an bar jama’a sun kada kuri’un su ba.

Wasu da-dama daga cikin shaidu sun fadawa kotu cewa, a cikin Unguwar Kwarbai ta Zariya da ake da akwatuna 26, ba a gudanar da zabe a mafi yawan wadannan rumfunan zabe ba.

Yahaya Abubakar, wanda ya yi wa PDP aiki a matsayin Wakili a zaben ya fadawa kotu cewa, sakamakon zaben da aka shirya dabam da abin da ke cikin takardar da ta fito daga hannun hukumar INEC.

Muhammad M. Amfani, ya tabbatarwa kotu cewa, ba a yi zabe a rumfa mai lamba 32 ba, sannan ya ce takardun da INEC ta fitar ba su kunshe da hatimin jami’an hukumar.

Haka kuma, Sadam Shehu ya ce, a matsayina na wakilin PDP ya tabbatar da cewa, a ranar 9 ga watan Maris ba ayi zabe a akwati mai lamba 001 ba.

Yanzu haka dai, Alkali Ibrahim Bako da sauran masu sauraraon karar sun karbi shaidu har 16, kuma lauyan PDP,Elisha Kurah ya ce  su na da wasu shaidu har guda 685.

Leave a Reply