Home Labaru Zaben Majalisa Ta 9: Ndume Ya Bukaci Kotu Ta Soke Kuri’ar Sirri...

Zaben Majalisa Ta 9: Ndume Ya Bukaci Kotu Ta Soke Kuri’ar Sirri Da Aka Kada

500
0

Tsohon shugaban masu rinjayen na majalisar dattawa Muhammad Ali Ndume ya bukaci babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta soke matsayar da majalisar ta dauka wajen kada kuri’ar sirri a lokacin zaben shugabannin majalisa ta 9.

A cikin takardar shigar da karar, lauyan sanata Ndume, Gboyega Adeyenmi, ya bukaci kotun da ta bada umurni na dakatar da majalisar daga tabbatar da kada kuri’ar sirri a matsayin tsarin zaben shugabannin majalisar.

A karar da ya Ndume shigar, an hada da magatakardar majalisar da kuma babban jami’in tsaron gudanarwar majalisar a matsayin wadanda ake tuhuma.

Ndume ya musanta cewa, Ikirarin da majalisar dattawa ta yi na tabbatar da yin amfani da kada kuri’ar sirri wajen zaben shugabannin majalisar ya sabawa dokokin majalisar na shekara ta 2015.

Ndume ya bukaci kotun da ta zantar da hukunci a kan abubuwa guda biyu, wanda suka hada da bukatar kotu ta bayyana idan sashe na 60 na kundin tsarin mulki ya ba majalisun tarayya  damar yi dokokin da tsare-tsare da za su ba wani mutum ko wani sashe na gwamnati damar da zai sauya dokokin.