Home Labaru Ilimi Sabanin Hankali: Kotu Ta Ce Ko Mutum Bai Yi NYSC Ba Zai...

Sabanin Hankali: Kotu Ta Ce Ko Mutum Bai Yi NYSC Ba Zai Iya Yin Takara

720
0

Wata Babbar kotun tarayya ta ce ba za a iya hana mutum yin takara don kawai bai yi bautar kasa ba.

Kotun ta yanke hukuncin ne, a lokacin da ta kori karar da tsohon dan majalisar dattawa Sanata Iyabo Anisulowo ya shigar a kan gwamnan Ogun Dapo Abiodun, bisa tuhumar cancantar shi ta tsayawa takara bayan bai yi bautar kasa ba.

A karar da aka shigar bisa tuhumar Abiodun da rashin yin bautar kasa, lauyan gwamnati ya roki kotu da ta yi watsi da karar, inda ya ce ba dole sai mutum ya yi bautar kasa zai iya yin takara ba.

Alkalin kotun, ya ce mai kara bai gabatar da shaidun da su ka nuna cewa wanda ake kara ya kai takardun bogi ga hukumar zabe ta kasa ba, sa’annan dokar hukumar yi wa kasa hidima ba ta ce dole sai mutum ya yi bautar kasa zai iya yin takara ba.

Leave a Reply