Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya musanta rahotannin da ke cewa ya bar wa sabuwar gwamnatin jihar bashin makudan kudade tare da bada wasu kwangiloli na bogi.
Abdulaziz Yari, ya ce babu gaskiya ko kadan a cikin bayanan, kuma an yi su ne kawai don a bata ma shi suna.
Mai magana da yawun sa Ibrahim Dosara ya shaida wa manema labarai cewa, zargin ba ya da tushe balle makama.
Idan dai za a iya tunawa, Kwamitin karbar mulki da Gwamna Matawalle ya kafa ne ya bankado wasu bayanai da su ka nuna gwamnatin Abdul-Aziz Yari ta bar bashin ‘yan kwangila da ya kai naira biliyan 251.
Ibrahim Dosara ya kara da cewa, sun yi mamakin yadda kwamitin bai shaida wa duniya cewa Abdul-Aziz Yari ya bar naira biliyan bakwai domin kammala aikin hanyoyin da aka fara a kananan hukumomi 14 na jihar ba.