Home Labaru Kasuwanci Tsantseni: An Yi Taro Kan Hanyoyin Sarrafa Kudade A Ma’aikatun Gwamnati

Tsantseni: An Yi Taro Kan Hanyoyin Sarrafa Kudade A Ma’aikatun Gwamnati

461
0
Ahmed Idris, Babban Akantan Gwamnatina Tarayya

A ranar larabar da ta gabata ne aka bude taron koli na Jami’an sarrafa kudade a ma’aikatu da hukumomin gwamnatocin tarayya da na jahohi a Kano, wanda ofishin babban Akanta Janar na Nijeriya ya shirya kan dabarun sarrafa dukiyar kasa.

Akantocin kudi na jahohi da daraktoci da sauran manyan Jami’an tafiyar da harkokin kudi a ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da takwararorin su na jahohi da birnin tarayya Abuja ne ke halartar taron na wuni uku.

Babban akantan gwamnatina tarayya Ahmed Idris, ya ce an shirya taron ne domin tattaunawa a kan yadda za a samar da sabbin hanyoyin da gwamnatocin jahohi da na tarayya za su bi domin samar da kudaden shiga.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC Ibrahim Magu, ya ja hankalin mahalarta taron su kiyaye da ka’idojin da doka ta shimfida wajen tafiyar da dukiyar al’uma.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Nasiru Yusuf Gawuna, ya ce aiwatarwa tare da sa ido sosai a kan tsarin asusun bai-daya ya ba gwamnatin jihar Kano damar like rariyar da kudade ke zirarewa a ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Leave a Reply