Home Labaru Sabani: ‘Yan Sanda Sun Sako ASD Da Dan Sa Da Sabon Surukin...

Sabani: ‘Yan Sanda Sun Sako ASD Da Dan Sa Da Sabon Surukin Sa

585
0

Hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna ta sako shahrarren dan kasuwa kuma tsohon shugaban kamfanin Peugeot Automobile Nigeria Ltd, Alhaji Sani Dauda ASD, bayan an tsares hi a kan aurar da diyar sa.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Alhaji Sani Dauda da dan sa Abdullahi Kumali da Alkalin kotun shari’a Sheikh Murtala Nasir Al-Misry sun isa gidajen su da misalin karfe 8:30 na safe.

Inda dai ba a manta ba, jami’an ‘yan sanda da ke yaki da ‘yan fashi da makami sun kama Alhaji Sani Dauda a kan rikici da ya barke bayan aurar da diyar sa da ya yi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, tsohon surukin Sani Dauda ya umarci ‘yan sanda su kama shi tare da dan sa Shehu Dauda da kuma alkalin kotun Musulunci da ke Magajin gari Murtala Nasir, wanda shi ne ya daura auren Naseeba da wani sabon miji.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, an daurawa Naseeba aure ne da wani mijin a ranar Asabar 9 ga watan Nuwamba, wanda hakan ya matukar bata wa tsohon mijin ta rai, ya kuma dauki matakin gani ‘yan sanda su kama mahaifin ta da sauran mutanen biyu da suka jagoranci daura auran.

Leave a Reply