Gwamnonin jam’iyyar APC sun nuna rashin jin dadin su a kan rikicin da ke cigaba da wanzuwa a jam’iyyar.
Gwamnonin dai sun bukaci shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole ya shirya taron shugabannin jam’iyyar cikin gaggawa ko ya sauka daga kujerar sa.
Kungiyar gwamnnoni ta bada wannan sanarwar ne sakamakon rikicin siyasar da ke tsakanin gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki da Oshiomhole da kuma sauran rikice-rikicen jam’iyyar a fadin Nijeriya.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Talatar da ta gabata ne jam’iyyar APC a jihar Edo ta dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole a jihar a kan zargin sa da hannu wajen rikicin jam’iyyar a jihar.
Hukuncin kuwa ya biyo bayan kuri’un da shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi 18 a jihar suka kada a kan dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa a jihar.
Takardar da aka ba manema labari a garin Abuja, wacce ta samu sa hannun daraktan kungiyar gwamnonin Salihu Muhammad. Lukman ta bukaci amsar tambayoyin da aka yi wa Oshiomhole na me ye musabbabin hana taron shugabannin jam’iyyar, wanda ya kamata a rika yi duk watanni hudu da dai sauran su.