Home Labaru Badakala: Kwamiti Za Ta Fallasa Masu Hannu A Fasa Bututun Mai

Badakala: Kwamiti Za Ta Fallasa Masu Hannu A Fasa Bututun Mai

425
0
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa

Rahoton kwamitin wucin-gadi na majalisar dattawa a kan fashewar bututun mai a ya nuna cewa, wasu ma’aikatan NNPC na hada kai da masu satar fetur domin aiwatar da ayyukan fasa bututun mai.

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya bayyana haka ne jim kadan bayan karbar  rahoton, inda ya kara da cewa duk jami’in da aka kama ya na hada kai da ‘yan ta’adda wajen fasa bututun mai zai yabawa aya zaki.

Ahmad Lawan ya kuma ce, ya zama dole kwamitin majalisar ya gayyaci matatar NNPC domin kara duba matakan tabbatar da tsaron bututun man fetur a fadin Nijeriya.

Shugaban ya kara da cewa, majalisar za ta gyara dokar cibiyar tantance nason man fetur ta kasa, domin ha na facaka da masu fasa bututu su ke yi, wanda hakan ke kawo gobara da mace-macen rayuka.

Sannan ya ce, kwamitin majalisar zai gayyaci ma’aikatar NNPC domin sanin wane mataki su ka dauka na kare bututun man fetur a cikin shekarun da suka gabata, da kuma wane matakai su ke amfani da su yanzu domin magance matsalar rasa biliyoyin dalolin.