Home Labaru Rikincin Zamfara: Buhari Zai Kaddamar Da Sabbin Jiragen Yaki Na Musamman

Rikincin Zamfara: Buhari Zai Kaddamar Da Sabbin Jiragen Yaki Na Musamman

305
0

Shugaban rundunar sojin sama na Nijeriya Air Marshal Sadique Abubakar ya ce nan bada dadewa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu jiragen yaki na musamman guda biyu domin kara bunkasa yaki da ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma.

Sadique ya bayda wannan tabbaci ne a lokacin bikin bude wasu sabbin gine-gine da aka yi a hedikwatar sojin sama da ke Maiduguri a jihar Borno, sannan ya bukaci dakarun soji da su kara kaimi wajen yin atisaye da suke saba gudanarwa domin yaki da ‘yan bindiga da kuma ayyukan ta’addanci.

Shugaban rundunar ya kuma ce, ya gamsu da irin nasarar da ake samu daga atisayen da dakarun soji da sauran jami’an tsaro ke gudanar wa domin tsarkake Nijeriya daga gurbatar da ta yi da ‘yan ta’adda.

Leave a Reply