Home Labaru Shugabancin Majalisa: Gwamna Shettima Ya Ce Za Su Yi Kokari Ndume Ya...

Shugabancin Majalisa: Gwamna Shettima Ya Ce Za Su Yi Kokari Ndume Ya Janyewa Lawan

260
0

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya ce, al’ummar jihar sa za su samu nasara a kan sanata Ali Ndume domin ya janyewa sanata Ahmad Lawan da jam’iyyar APC ta zaba matsayin dan takaranta na kujerar shugaban majalisar dattawa.

Shettima ya bayyana cewa, a matsayin su na masu biyayya ga jam’iyya, ya kamata su amince da zabin ta a kan Ahmad Lawan.

Yayin da ya ke zantawa da da manema labarai a lokacin da kwamitin yakin neman zaben sanata Ahmad Lawan su ka kai masa ziyara gidan sa da ke Abuja, gwamna Shettima ya ce sanata Ahmad Lawan ne sanatan APC mafi cancanta a wannan kujera.

Leave a Reply