Home Labaru Kiwon Lafiya Annoba: Cutar Kwalara Ta Kashe ’Yan Gudun Hijira 175 A Sansanin Su-MDD

Annoba: Cutar Kwalara Ta Kashe ’Yan Gudun Hijira 175 A Sansanin Su-MDD

312
0

Hukumar kula da harkokin kiwon lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce cututtuka da ke barkewa a sansanin ’yan gudun hijira na janyo asarar rayukan al’umma da dama.

Da ya ke magana a madadin jami’in kula da harkokin kiwon Lafiya na majalisar, Dakta Durkwa ya ce cutar Kwalara da Sankarau na matukar yin illa a sansanin ’yan gudun hijira, inda ko a shekarar da ta gabata an samu bullar cutar Kwalara a sansanonin ’yan gudun hijirar wanda hakn ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Ya ce, kimanin mutune 11,000 ne su ka kamu da cutar kwalara a kananan hukumomi 28 da ke yankin Arewa maso Gabas, inda sama da mutune 175 su ka mutu.

Idan dai ba a manata ba, hukumar kula da lafiya ta duniya ta dauki mata ma’aikatan kiwon lafiya su 454 da su ke aiki wajen fadakar da al’ummar karkara a kan abubuwan da ke janyo cutar Kwalara da Sankarau.

Durkwa ya kara da cewa, an kuma wayar da kan al’umma wajen rika kai ‘ya’yan su allurar rigakafin Kwalara da Poliyo, sannan a ba su magungunan da za su taimaka wa rayuwar su.

Leave a Reply