Home Labaru Rikicin Taraba: Buhari Ya Bukaci Hukumomin Tsu Gaggauta Daukar Mataki

Rikicin Taraba: Buhari Ya Bukaci Hukumomin Tsu Gaggauta Daukar Mataki

443
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gargadi hukumomin tsaron Nijeriya su gaggauta kawo karshen rikicin da ya mamaye jihar Taraba.

Yayin da ya yi tir da harin da ya auku a kauyen Kona na jihar Taraba, shugaba Buhari ya umurci dukkan hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki su gaggauta kawo karshen mummunan kalubalen da ya wuce gona da iri.

Shugaba Buhari ya yi gargadin cewa, gwamnatin sa ba za ta lamunci hare-haren da ke aukuwa a kan al’ummar jihar Taraba da sunan ramuwar gayya ba.

A cewar sa, babu wata kungiya da ke da lasisi ko hurumin kewaye mutanen da ba su ji ba su gani ba a zartar masu da ta’addancin mafi kololuwar zalunci babu gaira babu dalili.

Shugaba Buhari, ya kuma kalubalanci shugabannin da ke hudubar zaman lafiya a fili, amma su aikata sabanin haka yayin da su ka kebanta da mutane, wajen goyon bayan rura wutar kiyayya da hana ruwa gudu a tsakankanin al’umma.

Leave a Reply