Shugaban majalisar dattawa Sanata Lawan Ahmad, ya sake nada mutane uku a kan mukaman da su ka rike tun lokacin tsohon shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki.
Dukkan mutanen uku dais u na taimaka wa shugaban ne ta fuskar yada labarai.
Wadanda aka kuwa sun hada da Mohammed Isa a matsayin mai taimaka wa ta fuskar yada labarai, da Olu Onemola mai kula da kafofin sadarwa na zamani, da kuma Tope Brown Olowoyeye a matsayin mai daukar hotuna.
Sanata Lawan, ya kuma nada Misis Betty Okoroh a matsayin mataimakiya ta musamman akan kula da harkokin ofis, da kuma Okechukwu Nwankwoh mai kula da shirya tsare-tsaren duk wani taro na majalisar.